Jami’an kula da namun daji na Kenya sun fara kama kadoji a gabar tafkin Baringo, domin rage harin da kadojin ke kaiwa mutane da namun daji, yayin da tashin ruwan tafkin ke tilasta wa kadan kusantar gidajen jama’a.
Tafkuna da dama da ke yankin Rift Valley na Kenya sun cika da ruwa da ba a taba gani irinsa ba akalla rabin karni. Masana kimiyya sun danganta tashin ruwan da yawan ruwan sama mai tsanani da sauyin yanayi ke haddasawa.
- Yadda ƙungiyoyin fararen hula suka gudanar da gangamin goyon bayan janar Tiani
- Iran ta ce hare-haren Amurka sun kashe mutane huɗu a wajen bikin aure
- Jamus zata rufe ofishin jakadancin Rasha dake Bonn
A cewar bayanan hukumomi, hare-haren sun tilastawa dubban mutane barin gidajensu zuwa wuraren da suka fi tsayi, yayin da namun daji suka kara kusantar wuraren da mutane ke zaune.
Yayin da ake fargabar yanayin El Niño zai kara tsananta matsalar a cikin makonni masu zuwa, gwamnatin Kenya ta kaddamar da aikin mako guda a kusa da tafkin Baringo tun karshen makon da ya gabata, domin kama wasu daga cikin manyan kadojin da ke yankin tare da mayar da su wuraren da aka killace.