Hukumar kula da Babban Birnin Tarayya, FCTA, ta fara aikin share magudanan ruwa a fadin birnin Abuja, sakamakon ruwan sama mai ƙarfi da ya haddasa ambaliyar ruwa a wasu sassan babban birnin.

Aikin ya kunshi cire laka da shara da tarkace da sauran abubuwan da suka toshe magudanan ruwa, domin ba ruwa damar gudana yadda ya kamata tare da rage yiwuwar sake afkuwar ambaliya.

A yayin duba aikin da ake gudanarwa a kan titin Airport Expressway a ranar Alhamis, Mukaddashin Sakataren Hukumar Raya Babban Birnin Tarayya, FCDA, Richard Dauda, ya ce Ministan Abuja, Nyesom Wike, ne ya bayar da umarnin fara aikin.

Dauda ya ce matakin ya zama dole ne sakamakon yawan ruwan sama da aka samu a kwanakin baya, wanda ya janyo ambaliyar ruwa a wasu sassan Abuja tare da haifar da matsaloli ga zirga-zirgar ababen hawa da kuma rayuwar mazauna birnin.

Ya bayyana cewa share magudanan ruwa na daga cikin matakan da gwamnati ke dauka domin inganta tsarin kwashe ruwan sama a Abuja, musamman a wuraren da ke da tarihin fuskantar ambaliya.

Hukumar ta kuma mayar da hankali kan manyan hanyoyi da wuraren da ake yawan samun cunkoson ruwa, inda ake cire tarkacen da ke hana ruwa wucewa cikin sauƙi.

FCTA ta ce za a ci gaba da aikin a wasu sassan babban birnin, yayin da ake kira ga mazauna Abuja da su guji zubar da shara a cikin magudanan ruwa, saboda hakan na daga cikin abubuwan da ke haddasa toshewar hanyoyin ruwa.

Gwamnati ta ce haɗin kan jama’a na da muhimmanci wajen tabbatar da tsaftar magudanan ruwa da kuma rage illolin ambaliyar ruwa, musamman a wannan lokaci da ake samun ruwan sama mai yawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *