Babban Birnin Tarayya (Abuja) na ci gaba da kasancewa cikin jihohi 27 da Hukumar Kula da Harkokin Ruwa ta Najeriya (NiHSA) ta sanya ƙarƙashin gargaɗin yiwuwar ambaliyar ruwa, yayin da wa’adin gargaɗin da hukumar ta fitar ke ƙarewa a yau, 5 ga Agusta.

NiHSA ta ce ma’aunin ruwa na Izom da ke Kogin Gurara ya zarce matakin gargadi, lamarin da ke nuna yiwuwar ambaliyar ruwa a yankunan da ke kusa da koguna da sauran wuraren da ke fuskantar irin wannan barazana. Hukumar ta buƙaci mazauna wuraren da ke kan hanyoyin ruwa da filayen ambaliya su kasance cikin shiri, tare da komawa wurare masu tsaro idan ya zama dole.

Hukumar ta yi gargaɗin cewa idan matakin ruwan ya ci gaba da ƙaruwa, ambaliyar na iya shafar gidaje, hanyoyi, makarantu, kasuwanni, cibiyoyin lafiya, wuraren ibada da gonaki. Ta kuma gargadi jama’a da su guji ketare hanyoyi, gadoji ko rafukan da ruwa ya mamaye.

Gargaɗin ya zo ne bayan Hukumar ba da Agajin Gaggawa ta Babban Birnin Tarayya (FEMD) ta gama shirye-shiryen tunkarar ambaliya, inda ta buƙaci mazauna yankunan da ambaliya ke yawan shafa su kasance cikin shiri yayin da damina ke ci gaba.

Hukumar FEMD ta kuma shawarci mazauna Abuja su ci gaba da bin umarnin hukumomi tare da kai rahoton duk wani yanayin gaggawa ta hanyar lambar agajin gaggawa ta 112.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *