Dan wasan gaba na Amurka da Monaco, Folarin Balogun.

An cire sunan ɗan wasan gaba na Amurka Folarin Balogun daga cikin tawagar Monaco da za ta buga Gasar Conference League, bayan samun rashin tabbas game da makomarsa a ƙungiyar yayin da yarjejeniyar canza sheƙarsa zuwa Everton a wannan mako ya ruguje.

Kazalika, Balogun ba zai buga wasan da Monaco za ta fafata da Paris Saint-Germain a Gasar Faransa na ranar Jumma’a ba.

Monaco ta sanar cewa Balogun ya dawo atisaye tare da sauran ‘yan wasa, amma bai buga ko da wasa ɗaya ba daga cikin wasanni 4 da tawagar ta buga a wannan kakar.

Ɗan wasan gaba na Amurka ya kusa koma Everton kan kuɗi fam miliyan 40 a ranar Talata, wato ranar ƙarshe na rufe kasuwar saye da sayarwa na ‘yan wasa ta wannan bazara.

Balogun ya ƙi amincewa da kammala yarjejeniyar ne saboda bai gamsu da yadda Everton ta nuna rashin shakku game da sakamakon gwajin lafiyarsa, kamar yadda Daraktan Wasanni na Monaco, Thiago Scuro ya ce.

Monaco na cikin matsin lamba da ta sayar da Balogun, ko kuma wani daga cikin manyan ‘yan wasanta, domin ƙungiyar na buƙatar ganin ta cika ka’idojin kashe kuɗi na Gasar Faransa.

Scuro, ya ce har yanzu akwai yi wuwar Monaco ta sayar da ɗan wasan wadda aka haifa a New York, zuwa wata gasar wata ƙasa wanda har yanzu ba su rufe kasuwar hada-hadar ‘yan wasa ba, kamar gasar ƙasar Saudi Arabia, inda kasuwar za ta rufe a ranar 12 ga Oktoba.

Monaco za ta fara wasan matakin rukuni na Conference League a ranar 15 ga Oktoba, kuma sunan Balogun bai bayyana a cikin jerin sunayen da ƙungiyar ta bai wa UEFA wadda aka wallafa da daddare ranar Alhamis.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *