Rangers International, da Rivers United, da Shooting Stars, da kuma El-Kanemi Warriors, za su fara fafatawa a Gasar CAF ta kakar bana ta 2026/27 a ƙarshen wannan mako, inda duka tawagu huɗun za su buga wasa tsaƙanin ranar 5 zuwa 6 ga Satumbar 2026.
Zakaran Gasar Firimiyar Najeriya (NPFL) Rangers International da kuma ƙungiyar da ta zo na biyu a teburin, Rivers United ne za su wakilci Najeriya a Gasar Zakarun Nahiyar Afirka, yayin da Shooting Stars da kuma zakaran Gasar FA, El-Kanemi Warriors za su fafata a Gasar Confederation cup.
Rivers United za ta zama tawagar Najeriya ta farko da za ta buga wasa, inda za ta tafi Ivory Coast domin fafatawa da FC San-Pédro a filin wasa na Stade Auguste Denise ranar Asabar, 5 ga Satumba, da ƙarfe 4 na yamma agogon Nigeria.
-
Tawagar D’Tigress ta isa Berlin gabannin Gasar Ƙwallon Ƙwando ta Mata ta Duniya
-
FIFA ta amince da murabus ɗin Gusau da kuma sabon tsarin NSC
-
Gabriel Jesus ya koma Barcelona da
taka leda daga Arsenal
Haka kuma a ranar Asabar, Shooting Stars za ta fara na ta wasan a Gasar Confederation, inda za ta karɓi baƙuncin ƙungiyar ƙasar Tunisia, CS Sfaxien a filin wasa na MKO Abiola da ke Abeokuta, da misalin ƙarfe 4 na yamma.
A ranar Lahadi, 6 ga Satumba, Rangers za ta karɓi baƙoncin AS Sobemap daga Jamhuriyar Benin a Abeokuta, yayin da El-Kanemi Warriors za ta karɓi baƙuncin UDIB a filin wasa na Remo Stars da ke Ikenne. Za a buga dukkan wasannin biyu ne da misalin ƙarfe 4 na yamma.
Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan fara sabuwar kaka tua Gasar NPFL ta 2026/27, inda ake sa ran tawagu huɗun na Najeriya za su fara Gasar CAF ɗin da ƙarfi kuma cikin nasara.
Sai dai har yanzu batun filayen wasa da suka cika ƙa’idojin CAF, na ci gaba da zama babban ƙalubale inda hakan ya tilastawa wasu ƙungiyoyin Najeriya buga wasannin gida na Gasar CAF ba a asalin filin wasan su ba.