Tawagar D'Tgress

Zakaran Afirka, wato tawagar D’Tigress ta Najeriya, ta isa birnin Berlin na Jamus gabanin fara Gasar Cin Ƙwallon Ƙwando ta Mata ta Duniya.

Jakadan Najeriya a Jamus, Sanata Ita Enang, tare da wasu jami’an ofishin jakadancin Najeriya da ke babban birnin Jamus ne suka tarbi tawagar.

Zuwan nasu shi ne mataki na ƙarshe na shirye-shiryen gasar, wadda za a gudanar daga ranar 4 zuwa 13 ga watan Satumba na shekarar 2026 a Berlin.

D’Tigress, wadda ke riƙe da kambun zakaran Afirka bayan lashe Gasar FIBA ta mata ta AfroBasket karo na biyar a jere, za ta buga a rukunin B tare da Faransa, da Koriya ta Kudu da kuma Hungary.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *