Sojojin Operation FANSAN YAMMA sun ceto mutane uku da aka yi garkuwa da su a karamar hukumar Dandume ta jihar Katsina.
Lamarin ya faru ne a ranar 3 ga Satumba, 2026, bayan da mazauna yankin suka kai rahoton ayyukan ‘yan ta’adda da ake zargin suna gudana a kan hanyar Dandume zuwa Sheme.
A cikin wata sanarwa da Laftanar Kanal Aliyu Danja ya fitar, ya ce bayan samun kiran neman dauki, sojojin sashe na 2 na Rundunar Hadin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, tare da hadin gwiwar jami’an ‘yan sanda, sun gaggauta isa wurin.
Ya ce jami’an tsaron sun yi arangama da ‘yan ta’addan tare da yi musu luguden wuta, lamarin da ya tilasta musu tserewa cikin daji, inda suka bar mutanen da suka yi garkuwa da su.
A cewar sanarwar, sojojin sun gudanar da bincike a yankin, inda suka samu nasarar ceto mutane uku tare da kwato motoci biyu da ake zargin ‘yan ta’addan na amfani da su.
Laftanar Kanal Danja ya ce an mika mutanen da aka ceto da motocin da aka kwato ga Jami’in ‘Yan Sandan Sashen Dandume (DPO) domin daukar matakan da suka dace.
Ya kara da cewa sojojin na ci gaba da gudanar da sintiri mai karfi a yankin domin hana ‘yan ta’addan sake samun damar gudanar da ayyukansu.
Rundunar Operation FANSAN YAMMA ta yaba wa al’umma bisa ci gaba da ba jami’an tsaro hadin kai, tare da kira gare su da su kasance cikin taka-tsantsan tare da kai rahoton duk wani abu da suke zargi ga jami’an tsaro mafi kusa domin daukar matakin gaggawa.