Gwamnatin Najeriya ta musanta zargin cewa ta goyi bayan yunkurin juyin mulkin da ya gaza a Jamhuriyar Nijar.

Ma’aikatar Harkokin wajen Najeriya ta ce ikirarin da ake yaɗawa kan cewa Kungiyar Tattalin Arzikin Ƙasashen Afirika ta Yamma da Najeriya na da hannu a juyin mulkin da ya gaza a jamhuriyar Nijar ba shi da tushe.

Ministan Harkokin Wajen mai wakilci, Ambasada Sola Enikanolaye, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis.

Ya ce wasu bayanai da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta na koƙarin yaudarar jama’a da kuma bata sunan Najeriya.

Ministan ya ce Najeriya ƙasa ce mai son zaman lafiya, kuma mai kare tsarin mulkin dimokuraɗiyya da bin doka. Ya jaddada cewa Najeriya ba za ta taba goyon bayan haramtacciyar hanya ko sauya gwamnati ta hanyar da ba ta dace da kundin tsarin mulki ba, ko a wace ƙasa hakan ya faru.

Ya ce gwamnatin Najeriya ta riga ta bayyana matsayinta a wata sanarwar ma’aikatar harkokin wajen ƙasar mai lamba MFA/PR/2026/220, wadda aka fitar a ranar talatin ga watan Agusta.

A cikin sanarwar, Najeriya ta nuna matuƙar damuwa kan halin da ake ciki a Nijar tare da yin kira da a samu zaman lafiya da kuma komawar ƙasar cikin tsarin mulkin dimokuraɗiyya.

Najeriya ta ce tana kallon Nijar a matsayin makwabciya kuma ƙasa mai alaƙa da ita ta fuskar tarihi, al’adu da zumunci.

Don haka, abin da take muradi ga Nijar da yankin Sahel shi ne samun zaman lafiya, tsaro, dimokuraɗiyya da ci gaba.

Ministan ya ce amfani da ƙarfi, wajen warware rikicin siyasa ya saɓa da manufofin Najeriya na dogon lokaci na harkokin wajen ƙasar.

Ya kuma bayyana cewa duk da kasancewar Najeriya mamba mai kishin, Kungiyar Tattalin Arzikin Ƙasashen Afirika ta Yamma, ba daidai ba ne kuma karya ce a ce tana goyon bayan juyin mulkin soja.

Gwamnatin Najeriya ta buƙaci ‘yan ƙasar da ke gida da waje da su yi watsi da bidiyo da bayanan da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta da nufin haifar da rashin jituwa.

Ta kuma sake tabbatar da kudurinta na bin yarjejeniyar Kungiyar Tattalin Arzikin Ƙasashen Afirika ta Yamma, kan dimokuraɗiyya da shugabanci nagari da kuma tsarin Tarayyar Afirika na kin amincewa da duk wani sauyin gwamnati ta hanyar da ta saɓa wa kundin tsarin mulki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *