Wasu ‘yan ta’adda da ake zargi ‘yan Boko Haram ne sun yi kwanton bauna ga tawagar dan takarar kujerar gwamnan Jihar Borno na jam’iyyar APC, Injiniya Mustapha Gubio
Majiyoyi sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a yammacin ranar Alhamis, yayin da dan takarar da tawagarsa ke dawowa Maiduguri bayan kammala ziyarar godiya da suka kai garin Damasak da ke kan iyakar jihar.
Damasak na arewacin Borno, kuma yana da nisan kimanin kilomita 190 daga Maiduguri, babban birnin jihar.
- 2027: Obi, Falana da ADC sun nuna damuwa kan sahihancin zaɓe
- FCTA ta fara aikin share magudanan ruwa a Abuja
- Najeriya ta musanta goyon bayan yunkurin juyin mulkin Nijar
Wata majiya daga bangaren tsaro, wadda ta nemi a sakaya sunanta, ta bayyana cewa ‘yan ta’addan sun dasa nakiyoyi a kan babbar hanyar Gubio-Kareto zuwa Damasak.
Majiyar ta ce motar sulke ta ‘yan sanda da ke jagorantar ayarin ta taka daya daga cikin nakiyoyin, lamarin da ya haddasa fashewa.
Bayan fashewar, ‘yan ta’addan sun kai hari kan ayarin.
Sai dai wata rundunar hadin gwiwa ta jami’an tsaro, da ta kunshi sojoji, ‘yan sanda da mambobin Civilian Joint Task Force (CJTF), ta yi gaggawar mayar da martani tare da fafatawa da maharan.
Hanyar na zama wata babbar mashigar da ake zargin mayakan Boko Haram na amfani da ita wajen zirga-zirga daga maboyarsu da ke yankin tafkin Chadi zuwa Alagarno, dajin Sambisa da wasu sassan Jihar Yobe.