Tawagar D’Tigress ta Najeriya ta sha kaye da ci 99-81 a hannun Koriya ta Kudu a Gasar Cin Kofin Duniya ta Ƙwallon Kwando ta Mata ta 2026 a wasan su na farko da suka buga a ranar Jumma’a a Berlin, na ƙasar Jamus.

Wannan sakamako na nuni da cewa Najeriya ba ta taɓa samun nasara akan wata tawagar yankin Nahiyar Asiya ba a Gasar Cin Kofin Duniya ta FIBA ta Mata, sannan kuma ba ta taɓa samun nasara a wasan buɗe gasar ba.

D’Tigress ta yi ƙoƙari tun farkon wasan, amma ba ta iya kaiwa ga daƙile hare-haren da Koriya ta Kudu ke kai mata ba, inda tawagar Asiyar ta samu nasara akan ta.

Wannan shan kaye ya bar Najeriya da aiki mai yawa da za ta yi yayin da take shirin wasan ta na gaba da ƙasar Hungary.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *