Wata gobara da ta tashi a Kasuwar Kofar Wambai da ke jihar Kano, ta lalata gidaje shida, shaguna da wuraren ajiyar kaya.

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 9:43 na daren Juma’a a yankin Babban Layi, sashen Yan Robobi na kasuwar.

Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, ACFO Saminu Abdullahi, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar.

A cewar sanarwar, hukumar ta samu kiran gaggawa daga ɗaya daga cikin jami’anta, Usman Idris Fagge, bayan nan aka tura jami’an kashe gobara daga hedikwatar hukumar da tashoshin Rijiyar Zaki, Sabon Gari, Government House da Bompai.

Abdullahi ya ce gidajen da gobarar ta shafa sun haɗa da Gidan Alhaji Sani, Gidan Sani Muhammad, Gidan Alhaji Kwa Kwa, Gidan Alhaji Shafi’u da Gidan Alhaji Sulaiman.

Sanarwar ta ce jami’an kashe gobara sun gano cewa gobarar ta shafi kusan gidaje shida, waɗanda ke cikin wani ginin hawa biyu mai girman kusan ƙafa 120 da 125. Gini dai ya kasance kamfanin sarrafa robobi da kuma ajiyar kayayyaki.

Hukumar ta ce shaguna biyu da ke ƙasan ginin, wasu shaguna biyu da ke hawa na farko, ɗakunan ajiya shida da kuma wasu ɗakunan ajiya na wucin gadi guda huɗu da ke saman ginin sun samu matsala sakamakon gobarar.

Daraktan Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Alhaji Sani Anas, ya shawarci ’yan kasuwa da mazauna jihar da su ɗauki matakan kariya domin kauce wa aukuwar gobara.

Ya buƙaci ’yan kasuwa da mazauna gidaje da su sanya na’urorin gano gobara tare da samar da na’urorin kashe gobara masu aiki a gidajensu da wuraren kasuwancinsu, tare da bin ƙa’idojin kariya daga gobara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *