Shooting Stars ta garin Ibadan ta samu nasarar lallasa CS Sfaxien na ƙasar Tunisia da ci 1-0 a Gasar CAF Confederation Cup da suka buga a filin wasa na MKO Abiola dake Abeokuta, a ranar Asabar.

Ɗan wasa Lucky Emmanuel ne ya zura ƙwallon da ya bambanta tsakanin ƙungiyoyin biyu a minti na 25 da fara wasa.

CS Sfaxien ta matsa lamba sosai bayan dawowa daga hutun rabin lokaci domin farke ƙwallon da aka zura mata amma mai tsaron ragar Shooting Stars ya ƙi yarda da hakan.

Kazalika, masu tsaron gidan Shooting Stars sun kasance cikin shirin daƙile duk wani harin da aka yi ƙoƙarin kai musu.

Shooting Stars ta kuma samu damar ƙara zura wata ƙwallon amma ta kasa amfani da damar da ta samu.

Wannan nasara ta ɗora Shooting Stars akan gaba gabannin wasan zagaye na biyu na wannan gasa da za su buga a mako mai zuwa a ƙasar Tunisia.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *