Kamfanonin Hybrid Motors Nigeria da Launch Design Shanghai na China sun ce sun lashi takoni kafa masana;antun kera motoci masu amfani da makamashin lantarki a Abuja da Legas ne domin samar da ayyukan yi da bunkasa ci gaban zamani a Najeriya.

Kamfanonin sun bayyana hakan ne yayin rattaba hannu a kan wata yarjejniyar hadin gwiwa a birnin Shanghai na China wadda ta tanadi samar da motoci kirar Acely a Najeriya.

Da yake jawabi yayin sa hannun, Shugaban kamfanin Hybrid motors Nigeria, Jubril Arogundade, ya ce hadin gwiwar wani matakin kawo sauyi ne na kafa wa Najeriya masana’antar kera motoci ta-gani-ta-fada a duniya.

“Da kirkirar Acely, muna nuna cewa ’yan Najeriya za su iya hararo motocin da za a yi alfahari da su a duniy, su zayyana, su kuma kera su a Najeriya don ’yan Najeriya”, inji shi.

Ya kara da cewa hadin gwiwa da Launch Design Shanghai zai kawo kwarewa irin ta kasa-da-kasa ga harkar kirkirar ababen hawa ta gida a Najeriya.

Za dai a kafa masana’antun ne a Shiyyar Masana’antu ta Centenary Economic City da ke Abuja da kuma a kusa da Babbar Tashar Jiragen Ruwa ta Lekki da ke Legas.

Ana sa ran masana’antar ta Abuja za ta rika samar da motoci masu amfani da nau’in makamashi fiye da daya 20,000 duk shekara don sayarwa a Arewa da sauran kasashen Yankin Sahel.

Ita kuwa masana’antar ta Legas za ta kera motoci 50,000 duk shekara don sayarwa a kasashen Afirka ta Yamma da suka hada da Ghana da Jamhuriyar Benin da Togo da kuma Ivory Coast.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *