Lionel Messi ya cimma yarjejeniyar farko don zama sabon mamallakin kungiyar CD Eldense, dake fafata wasa a mataki na biyu a kasar Spaniya, kamar yadda kungiyar ta tabbatar da hakan a ranar Laraba.
“A halin yanzu, an dakatar da kammala wannan ciniki har sai an cimma dukkan sharudan doka da na kwantaragi na karshe, ciki har da tsarin fitar da bayanan da suka dace, da kuma samun izini daga kwamitin ƙoli na wasanni na CSD,” kamar yadda Eldense ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.
Ɗan wasan gaban na Inter Miami yana daf da kammala yarjejeniyar siyan kaso 100 na hannun jarin Eldense, wadda ƙungiyar zuba jari ta Colombia mai suna TH Soluciones Group SAS ke mallaka, wadda ita ce babbar mai hannun jari a yanzu.
- Yaya Touré ya kafa tarihi a gasar zakarun Turai
- NFF ta naɗa Eguavoen kocin wucin gadi na Super Falcons
- Najeriya za ta kara da Russia a wasan sada zumunta
Messi mai shekaru 39 yana shirin mallakar ƙungiya ta biyu a Spaniya bayan sayen UE Cornella dake buga wasa a mataki na 5 a Spaniya a ranar 16 ga watan Afrilu a farkon wannan shekarar.
Haka kuma ana sa ran zai samu kason hannun jari a ƙungiyarsa ta yanzu Inter Miami bayan ƙarewar kwantaraginsa na wasa.
Rahotanni daga Spaniya sun ce ana sa ran za a kammala yarjejeniyar sayen Eldense cikin kwanaki masu zuwa.
Sai dai ƙungiyar ba ta bayar da takamaimiyar ranar da za a kammala cinikin ba.