Ministan Yada Labarai na Najeriya Alhaji Mohammed Idris, ya jaddada muhimmancin zaman lafiya da haɗin kan ƙasa, inda ya bayyana cewa alhakin gina Najeriya da kare makomar ta ya rataya a wuyan kowane ɗan ƙasa, ba tare da nuna bambancin addini ko ƙabila ba.
Ministan, ya bayyana hakan ne ranar Laraba a Abuja, yayin da yake jawabi a wurin babban taron Shugabannin Coci na Ƙasa, wato (Charismatic Bishops Conference), taron da ya haɗa shugabannin coci daga jihohi 36 na ƙasar da Birnin Tarayya.
Malam Mohammed Idris, ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su riƙa gudanar da siyasa bisa tsari, ba tare da cin zarafin ra’ayin kowa ba.
- Gwamnatin Tarayya ta ba da umarnin biyan Lakcarori alawus din ‘CATA’
-
NDLEA ta cafke wani da ake zargi da safarar hodar Iblis mai nauyin kilogiram 49.70
Ya ƙara da cewa, ko da mutum ba ya goyon bayan gwamnati ko shugabannin da ke kan mulki a yanzu, hakan bai ba shi damar rusa haɗin kan ƙasa ko shuka ƙiyayya da gaba tsakanin al’umma ba.
“Zaɓe wani abu ne na ɗan gajeren lokaci, amma ita ƙasar zata wanzu bayan shuɗewar zaɓuka, gwamnatoci, da jam’iyyun siyasa. Shi ya sa babbar hanyar da za mu bi ita ce mu kiyaye alakar mu, mu zuba jari a fannin ilimi da ƙwarewar matasan mu, domin su gina kyakkyawan tsari da ya dace da rayuwar su a gaba,” in ji Ministan.
Haka zalika, ya yabawa jagororin taron da suka zakulo mahalarta daga sassan ƙasar, inda ya yi fatan shawarwarin da aka yanke za su haifar da ɗa mai ido ta fuskar gina al’umma nagartacciya.
Da yake magana kan sauye-sauyen da gwamnatin ke aiwatar wa, Ministan ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu yana tsaye tsayin daka wajen cika alƙawuran da ya ɗauka na inganta rayuwar ‘yan ƙasa.
Ya kuma mika godiya ta musamman ga hukumomin tsaron ƙasar, bisa ƙoƙarin da suke yi dare da rana wajen kiyaye rayuka da dukiyoyin al’umma.
A ƙarshe, Ministan ya roƙi Allah da ya ci gaba da baiwa shugabannin addinai da na ƙasa baki ɗaya hikima da kwarin gwiwar gudanar da ayyukan su bisa adalci da kishin ƙasa.