Kamfanin Mai na NNPC Retail ya ƙaddamar da wani gidan mai na zamani a Abuja, inda masu hulɗa dashi zasu iya biyan kuɗin adadin mai da ababen hawan su zasu sha sannan su zuba da kansu, ba tare da jiran wani yayi musu hakan ba.
NNPC Retail wani ɓangare ne na kamfanin, mai kulawa da yadda ake siye da siyar da kayayyakin kamfanin kai tsaye ga mabuƙata.
An ƙaddamar da tashar ne ranar Alhamis, 10 ga Satumba, 2026, wadda ke aikidare da rana kamar yadda kamfanin ya sanar.
- Dillalan Man Fetur sun yi barazanar rufe gidajen mai idan…
- Afirka na shirin kafa nata ma’aunin farashin man fetur – NMDPRA
- IPMAN: Sayen fetur kai tsaye daga matatar Ɗangote zai rage farashin lita a gidajen mai
Yace gidan man na aiki da manhajar NNPC Retail, da za ta baiwa mutane zaɓin adadin man da biya cikin sauƙi, sai kuma damar zuba man ga wanda ya siya kai tsaye daga famfo ba tare da wani ma’aikaci ba.
Sai dai kamfanin ya ce, ma’aikata za su ci gaba da kasancewa a tashar domin taimaka wa mutanen da ba su iya amfani da manhajar ko tsarin zuba mai da kansu ba.
Baya ga man fetur, tashar na samar da dizal da iskar gas na girki, cajin motocin lantarki, wanke motoci, gyaran ababen hawa da sayar da baƙin.
Tashar tana da famfunan man fetur guda 16 da kuma famfunan dizal guda biyu, yayin da aka samar da wurare shida domin cajin motocin lantarki.
Kamfanin ya kuma ce yana shirin samar da irin wannan tsarin zuwa sauran sassan ƙasarnan, cikin watanni shida masu zuwa.
A cewar kamfanin, ana sa ran samun kusan tashoshi huɗu zuwa biyar a Abuja, yayin da za a samar da biyu a Kano.