Ƙasar Aljeriya, ta rufe sararin samaniyarta ga jiragen sama na fasinja da na soji da ke fitowa daga Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), bayan ta yanke hulɗar diflomasiyya da Abu Dhabi sakamakon ƙaruwar rashin jituwar da ta daɗe tana tsakanin ƙasashen biyu.

Ma’aikatar Tsaron Aljeriya, ta ce dokar ta fara aiki daga daren ranar Juma’a 11 ga Satumba, ko da yake yake an karawa jiragen yan kasuwar Abu-Dhabin karin wa’adin nan da ƙarshen shekarar 2026, su cigaba da sauka da tashi daga filin jirgin sama na Houari Boumediene da ke Algiers.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Aljeriya, ta ce ta sha gargadin Abu Dhabi kan irin matakan da take ɗauka kan abin da ya shafi Arewacin Afirka musamman ƙasashen yankin Sahel, amma ta ce UAE ta yi kunnen ƙashi da shawarar.

Algiers, ta bai wa jakadan UAE wa’adin sa’o’i 48 domin ya bi wannan mataki.

Geoff Porter, Jami’i ne a wani kamfani dake bincike akan tsaro da zuba jari mai suna (North Africa Risk Consulting), ya ce Aljeriya ta kasance tana ƙoƙarin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.

A cewar  rahoton kamfanin na NARC, rawar da UAE ke takawa a yankin na Sahel na zamewa makomar yankin kafar ungulu ta fuskokin zuba jari da zaman lafiya mai dorewa.

Porter ya yi nuni da goyon bayan Abu Dhabi ga jagoran dakarun LNA Khalifa Haftar, dake jagorantar gabashin Libya. Haka nan ita ke marawa rundunar Dakarun RSF a Sudan baya, da kuma rahotannin cewa akwai sansanin jiragen sama marasa matuƙa a ƙasar Mauritania da ke makwabtaka da Aljeriya, dake haifar da barzanar tsaro ga Algiers.

kazalika Aljeriya na ci gaba da adawa da daidaita hulɗa da Isra’ila ta ƙarƙashin yarjejeniyar Abraham Accords, wadda UAE ta amince da ita. Aljeriya na ganin bai kamata a kulla irin wannan hulɗa ba kafin a kafa ƙasar Falasɗinu mai cin gashin kanta.

Daga cikin matakan da Aljeriya ta ɗauka akwai fara aikin soke yarjejeniyar zirga-zirgar jiragen sama tsakanin ƙasashen biyu ta shekarar 2013.

A shekarar da ta gabata, Shugaban Aljeriya, Abdelmadjid Tebboune, ya ce dangantakar ƙasar sa da dukkan ƙasashen Larabawa na yankin Gulf tana da kyau, in-ban-da wata ƙasa guda, abin da ake ganin yana nuni ne ga UAE.

Aljeriya na kallon irin waɗannan matakai a matsayin tsoma baki kan harkokin yankin da ke ƙarƙashin tasirin ta, tare da yiwuwar zama barazana ga tsaron ƙasarta.

ko a kwanakin baya sai da Aljeriya ta tura jiragen yaki zuwa Jamhuriyar Nijar, bayan wani yunkurin kifar da gwamnati da ba’a samu nasarar sa ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *