Tambarin Hukumar NFF

Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Najeriya, NFF, ta zaɓi wakilai 27 ciki har da shugabanni 9 na Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Jihohi, domin yin taro da jami’an Hukumakar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya, FIFA, da takwararta ta Afirka, CAF, a Abuja ranar Litinin, 14 ga Satumba.

Taron yana daga cikin tattaunawa da ake yi domin magance rikicin jagoranci a Hukumar NFF da kuma samar da gyare-gyare sakamakon murabus ɗin tsohon Shugaban NFF, Ibrahim Gusau, da dukan Kwamitin Zartarwa nasa da kuma Sakatare Janar, Mohammed Sanusi.

Ana sa ran tawagar FIFA da CAF za su zo Najeriya ne domin ganawa da manyan masu ruwa da tsaki a harkar kwallon kafa da kuma tantance gaskiyar halin da ake ciki game da tsarin gyare-gyaren da aka tsara, ciki har da shirin kafa kwamitin riko na gudanarwa na NFF.

Ana kuma sa ran taron zai ba hukumomin kwallon kafa na duniya damar zantawa da manyan wakilan sassa a kwallon kafar Najeriya da kuma tattara ra’ayoyi da za su iya yin tasiri kan mataki na gaba na tsarin gyare-gyaren.

A cewar wasikar NFF mai kwanan wata 9 ga Satumba, 2026, wadda Sakatare Janar na riko Emmanuel Ikpeme ya sanya wa hannu, shugabanni 9 ne kawai daga cikin shugabanni 37 na Hukumar Kwallon Kafa na Jihohi za su halarci taron da aka tsara za a yi shi a Continental Otal na Abuja.

Har wayau, an gayyaci Shugaban Kungiyar Koca-kocai da sauran wakilai 2 — daya daga Arewa, daya kuma daga Kudu.

Sannan kuma, Kungiyar Alkalan Wasa da Kungiyar ‘Yan Wasanni za su tura shugabanninsu da wakilai 2, inda za a dauko wakilci daya daga kowane yanki biyu na kasar.

Shugabancin shirya Gasar Kwararru na cikin gida ma za su tura da wakilci.

Ana sa ran Hukumar NPFL, da NWFL, da NNL da kuma NLO kowace za ta tura da Babban Jami’in Gudanarwa tare da wakilan kungiyoyi 2 — daya daga Arewa, daya daga Kudu.

Ikpeme ya bayar da umarnin a mika sunayen dukkan wakilan da aka zaba zuwa Sakateriyan NFF cikin sa’o’i 48.

Rikicin jagoranci na NFF ya biyo bayan murabus din Gusau da dukan Kwamitin Zartarwa, lamarin da ya haifar da tambayoyi kan yadda ake gudanar da hukumar da kuma makomar zaben da aka tsara gudanarwa a baya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *