Cristiano Ronaldo ya ƙara matso kusa a ƙoƙarin cimma burinsa na zura ƙwallaye 1,000 yayin da ya ci ƙwallo ɗaya a wasan da Al Nassr ta fafata da Abha a Gasar Saudiyya na ranar Laraba.
Wannan ƙwallo da ya ci ita ce ta 3 ga Ronaldo a wasanni 5 da ya buga wa Al Nassr a kakar bana ta 2026-27 ta Gasar Saudi Pro, kuma ita ce ƙwallo ta 132 da ya ci wa ƙungiyar tun bayan dawowarsa ƙasar Saudiyya.
Ɗan wasan gaban na ƙasar Portugal mai shekaru 41 ya zura ƙwallon ne a minti na 22.
- Lionel Messi ya cimma yarjejeniyar sayen kungiyar CD Eldense ta kasar Spaniya
-
Yaya Touré ya kafa tarihi a gasar zakarun Turai
-
NFF ta naɗa Eguavoen kocin wucin gadi na Super Falcons
Wannan ƙwallon ta ƙara yawan jimillar ƙwallayen da Ronaldo ya ci a dukkan fafatawa zuwa 979, ma’ana ya rage masa ƙwallaye 21 kacal don ya kai 1,000.
Wannan lamarin na ci gaba da jan hankali ne bayan Ronaldo ya sanar da cewa kakar 2026-27 ka iya zama ƙarshe a gare shi a matsayin ƙwararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa.
Har wayau, ƙwallon ta ƙarfafa matsayin Al Nassr a saman teburin Gasar Saudiyya inda ƙungiyar ta kamo Al Hilal da yawan maki 15 kowanne.
