Cibiyar Yaƙi da Laifukan Kafar Intanet ta Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta kama wata mata da ake zargin yaɗa wata sanarwa ta ƙarya da ke cewa kamfanin fintech na OPay Digital Services Limited zai rufe ayyukansa a Najeriya.
An kama wacce ake zargin ne a ranar 4 ga Satumbar 2026, sakamakon binciken da jami’an ’yan sanda suka gudanar game da wannan sanarwa da ta yaɗu a kafar sada zumunta ta X, wadda aka fi sani da Twitter.
An ruwaito cewa sanarwar ta samu kusan mutane 572,000 da suka gani cikin ‘yan mintoci bayan an buga ta.
- ‘Yan sanda sun kama jami’in bogi a Kano, sun ƙwato kayan sarki da Naira 300,000
- ’Yan sandan FCT sun kama matar da ake zargi da zuba wa makwabciyarta ruwan zafi
- NDLEA ta cafke wani da ake zargi da safarar hodar Iblis mai nauyin kilogiram 49.70
Rundunar ‘yan sandan ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, CSP Ani Iniedu, ya fitar a ranar Alhamis.
A cewar ’yan sanda, an tsara sanarwar ƙaryan ne kamar wadda ta fito a hukumnce daga kamfanin OPay.
Sanarwar bogin ta yi ikirarin cewa za a rufe ayyukan OPay daga ranar 1 ga Satumba, lamarin da ‘yan sanda suka ce zai iya haifar da ruɗani ga jama’a da kuma haifar da damuwa ga abokan ciniki.
‘Yan sandan sun ce har yanzu suna ci gaba da bincike don gano yadda aka ƙirƙiri wannan sanarwa ta ƙarya, da kuma gano ko akwai wasu mutane da suke da hannu cikin lamarin.
Sun ƙara da cewa bayan kammala bincike, za su gurfanar da wacce ake zargin da duk wanda aka samu da hannu a cikin lamarin a gaban kotu.