Shugabannin ƙasashen BRICS sun yi kira a ranar Asabar ga ƙasashen duniya masu ci gaba da su samar da tallafin kuɗi ga ƙasashe masu tasowa domin kare halittu da kuma tabbatar da ɗorewar amfani da albarkatun halittu.
Shugabannin sun ce a saboda haka, ƙasashen da suka ci gaba ya kamata su taimaka wajen ƙarfafa ƙwarewa da kuma bunƙasa fasaha a ƙasashe masu tasowa.
Sun bayyana hakan ne a cikin yarjejeniyar New Delhi ta 2026, a taron kungiyar da ake gudanarwa a yanzu haka a India.
Sanarwar ta kuma jaddada muhimmiyar rawar da kowane irin daji, ciki har da dazuzzukan yankunan sanyi da na wurare masu zafi, ke takawa wajen kare halittu da magudanan ruwa da kuma ƙasa.
- Ƙasashen BRICS zasu haɗa gwiwa a fannin lafiya da yakar cutar tarin fuka
- BRICS ta ce Bankin NDB zai taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa tattalin arzikin ƙasashe masu tasowa
- Taron BRICS: Shugaban China ya bukaci mambobi su samar da zaman lafiya a Yammacin Asiya
Haka kuma, shugabannin sun yi maraba da amincewa da wasu takardu guda biyu da suka shafi inganta muhalli da maido da lalatacciyar ƙasa bisa tsarin shimfidar wuri, da kuma fahimtar bai ɗaya kan shirin tunkarar gobarar daji da mayar da martani gare ta a tsakanin ƙasashen BRICS.
Takardar farko ta tattara ƙwarewa da kyawawan hanyoyin aiki da manufofi daga ƙasashen BRICS wajen magance matsalolin da ke da alaƙa da lalacewar ƙasa da kwararowar hamada da asarar halittu da kuma sauyin yanayi.
Yayin da ta biyu ke bayyana hangen nesa na bai ɗaya kan yadda za a tafiyar da harkokin gobarar daji, wanda ya haɗa da rigakafi da shiri, bayar da gargaɗin farko da ɗaukar matakin gaggawa, da kuma ayyukan ceto da farfaɗowa bayan gobara.