Mutane biyu sun jikkata, yayin da wani masallaci da wasu gine-gine suka lalace bayan wani makami da mayakan Houthi na Yemen suka harba ya faɗa yankin Jazan da ke kudancin Saudiyya a ranar Asabar.
Hukumar tsaron farin kaya ta Saudiyya ta ce jami’an ceto sun kai ɗauki a lardin Al-Tuwal, bayan makamin ya faɗa yankin, inda har ila yau ya lalata wasu motoci.
- Dakatar da yaki: Iran da Hadaddiyar Daular Larabawa sun goyi bayan BRICS
- Ku samar da kuɗaɗe don kare halittu – BRICS ga G7
- Ƙasashen BRICS zasu haɗa gwiwa a fannin lafiya da yakar cutar tarin fuka
Wani kakakin Hukumar tsaron farin kaya ya bayyana kai hari kan wuraren fararen hula a matsayin “mummunan take dokokin jin kai na ƙasa da ƙasa,” yana mai cewa hukumomi sun ɗauki matakan da aka tanada domin tunkarar irin waɗannan hare-hare.
Harin ya zo ne a daidai lokacin da ake samun ƙarin tashin hankali a fannin tsaro a Saudiyya, sakamakon jerin hare-haren makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa da mayakan Houthi suka kai a kudancin ƙasar cikin ‘yan kwanakin nan.
A ranar Talata, ƙungiyar ta kai hare-hare kan wuraren fararen hula da na tattalin arziki a biranen Abha da Khamis Mushait da Jazan da Najran, inda mutane 73 suka jikkata, ciki har da mata da yara.