Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima ya jaddada aniyar Nijeriya wajen gudanar da aiki tare da Kungiyar Kasuwanci ta Duniya (WTO) da kuma tsarin kasuwanci na bangarori daban-daban na duniya.

Shettima ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin wani taro tsakaninsa da Darakta Janar na kungiyar WTO, Dr Ngozi Okonjo-Iweala, a birnin New Delhi na kasar Indiya.

Taron ya gudana ne a gefen taron koli na shugabannin kungiyar BRICS da ke gudana a halin yanzu.

Shettima ya ce babu wata kasa da za ta iya samun dorewar arziki ta hanyar ware kanta daga sauran kasashen duniya.

Ya ba da tabbacin cewa Nijeriya za ta ci gaba da goyon bayan kokarin WTO na karfafa huldar kasashe daban-daban da kuma inganta hadin gwiwa tsakanin kasashen duniya.

“Na yi amanna cewa duniya ta fi karfin kasa guda daya. Za mu ci gaba da goyon bayan WTO wajen fafutukar ciyar da tsarin hadin gwiwar kasashe daban-daban gaba,” in ji shi.

Shettima ya jaddada cewa a halin yanzu kasashe suna da alaka mai karfi da juna kuma suna bukatar juna domin cimma dorewar ci gaban tattalin arziki.

“Alal hakika mu iyali daya ne a duniya kuma muna da alaka da juna. Ba za ka iya ware kanka daga al’ummar duniya ba,” in ji shi.

Haka zalika, Mataimakin Shugaban Kasa ya bayyana hijira a matsayin daya daga cikin muhimman abubuwan da ke tuka ci gaba da sauye-sauye masu kyau, da habakar tattalin arziki a kasashe daban-daban.

Ya ce a tarihi, ‘yan ci-rani sun ba da gudummawa mai tarin yawa wajen ci gaban kasashe da manyan birane a fadin duniya.

Ya ce: ‘yan ci-rani ne ke gina kasashe. Hatta birane ma mutanen da suka fito daga waje ne ke gina su, ba yan gari kawai ba’.

“Wannan yana nuna mana cewa muna da abubuwa da dama da za mu amfana da su daga hijirar mutane a fadin duniya.”

Ya kawo al’ummar Nijeriya da ke zaune a kasashen waje a matsayin shaida ta gudummawar da yan ci-rani za su iya bayarwa ta hanyar ilimi da kasuwanci, da kwarewa a fannoni daban-daban.

Shettima ya ce ‘yan Nijeriya da ke zaune a kasashen waje suna ci gaba da nuna kwarewa a fannoni daban-daban da kuma ba da gudummawa mai kyau ga kasashen da suke zaune.

Ya ambaci binciken da Cibiyar Bincike ta Pew (Pew Research Centre) ta gudanar na kwanan nan kan bayanan Hukumar Kididdiga ta Amurka (US Census Bureau) na shekarar 2024 game da bakin fata ‘yan asalin Nijeriya da ke zaune a Amurka.

“Kashi 67 cikin 100 na bakar fata ‘yan asalin Nijeriya da aka haifa a Nijeriya wadanda shekarunsu suka kai 25 zuwa sama a Amurka suna da akalla digirin farko.

“Wannan shi ne mafi kololuwar rabo tsakanin manyan kungiyoyin bakar fata ‘yan ci-rani da aka yi bincike a kansu,” in ji Mataimakin Shugaban Kasa.

Shettima ya jinjina wa Okonjo-Iweala dangane da yadda take jagorantar kungiyar WTO, kuma ya bukace ta da ta ci gaba da yin amfani da kwarewarta wajen ciyar da ci gaban duniya gaba.

“Kina gudanar da aiki mai kyau kwarai da gaske a WTO, amma har yanzu kina da abubuwa da dama da za ki gudana wa bil’adama,” in ji shi a gare ta.

Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa Okonjo-Iweala ita ce mace ta farko kuma ‘yar Afrika ta farko da ta rike mukamin Darakta Janar na WTO.

Ta fara aiki a wa’adinta na biyu na tsawon shekaru hudu a matsayin Darakta Janar a watan Satumban 2025, sakamakon sake nada ta da aka yi domin ta jagoranci kungiyar.

A halin da ake ciki, an tsara Shettima zai gabatar da damar kawance da zuba jari na kasashen waje da ke Nijeriya ga shugabannin BRICS a ranar Lahadi.

Gabatarwar tasa za ta kasance wani bangare na tattaunawar Nijeriya a taron koli na shugabannin BRICS da ke gudana a New Delhi.

Taron kolin yana gudana ne a karkashin taken, ‘Gina Gwagwarmaya, Sauye-sauye Masu Kyau, Hadin Gwiwa da Dorewa.’

Ana sa ran Shettima zai fito da Tsarin Sabunta Fata (Renewed Hope Agenda) na Shugaba Bola Tinubu da kuma mayar da hankalinsa wajen samar da damammaki masu dorewa ga yan Nijeriya.

Haka zalika zai bayyana gyare-gyaren da nufin fadada ababen ofisoshi da karfafa juriyar tattalin arziki, da inganta ci gaban da bangaren masu zaman kansu ke jagoranta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *