Landan ta sha kaye a hannun Nairobi wajen neman karɓar baƙuncin Gasar Motsa Jiki ta Duniya ta 2029.

An tabbatar da wannan matakin ne yayin taron Majalisar Gudanarwa ta Hukumar Wasannin Motsa Jiki ta Duniya da aka yi a Budapest.

Hakan kuma na nufin wani birni na Afirka ne zai karɓi baƙuncin gasar a karon farko.

Shugaban Gudanarwar Hukumar Wasannin Motsa Jiki ta Duniya, Sebastian Coe, ya ce Nairobi ta gabatar da buƙata “mai jan hankali da cike da armashi.”

“Mun yi sa’ar samun ƙasashe huɗu da suka nuna buƙatar karɓar baƙuncin wasan na shekarar 2029 da 2031, amma hakan bai zo mana da sauƙi ba,” in ji Coe.

“Da wannan hukuncin da muka yanke a yau, muna ci gaba da cika manufarmu ta bunkasa wasan guje-guje da tsalle a fadin duniya ta hanyar bayar da damar karbar bakuncin Gasar Motsa Jiki ta Duniya a nahiyoyin Asiya, da Afirka da kuma Turai.

“Nairobi ta gabatar da tayi mai jan hankali da cike da armashi, kuma kai gasar zuwa Afirka a karon farko zai zama babban tarihi.”

Filin wasa na Landan Stadiya, gida ga kungiyar West Ham United, shi ne filin da aka tsara zai karbi bakuncin na Burtaniya.

An kuma yi amfani da filin wasan a Gasar Olympics ta 2012 da kuma gasar London Diamond League ta shekara-shekara, da kuma lokacin da birnin ya karbi bakuncin gasar ta Duniya a 2017.

A can baya, Nairobi, Babban Birnin Kenya, ta gabatar da buƙatar karɓar baƙuncin gasar ta 2025 amma ta sha kashi a hannun Tokyo.

Ana gyara filin wasa na Kasarani da ke birnin gabanin Gasar Cin Kofin Nahiyar Afirka (AFCON) ta 2027, wanda ya karfafa hujjarta a matsayin filin karbar bakuncin gasar.

Kenya ta ƙare a matsayi na biyu a teburin lambobin yabo a gasar 2025, inda ta lashe lambobin zinare bakwai da jimillar lambobin yabo 11.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *