Tawagar mata ‘yan ƙasa da shekaru 17 ta Najeriya, Flamingos, ta fara Gasar WAFU B na ‘Yan Mata ’Yan ƙasa da shekaru 17 na 2026 cikin salo mai ƙayatarwa da nasara yayin da ta lallasa Jamhuriyar Nijar da ci 5-0 a Yamoussoukro, a ranar Laraba.
Flamingos ta nuna karfinta tun daga busar farko, inda ta mamaye wasan da kuma sarrafa tafiyar wasan.
Kyaftin Harmony Chidi ita ta fara zura ƙwallo a minti na 16.
Sannan Awawu Bashiru ta kara kwallo ta biyu bayan matsin lambar da tawagar Najeriya ta dade ta na kai wa, yayin da mai tsaron ragar Najeriya Onyiyechi Opara ba ta ma san ana yi ba har aka gama minti 45 na farko.
-
Messi zai sake buga wa Argentina wasa kafin yin bankwanan ƙarshe
-
Wasan Najeriya da Ingila: Abubuwan da ya kamata ku sani
-
Kwallon Raga: Najeriya ta samu nasara ta farko a Gasar Ƙasashen Afirka ta 2026
Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci, Flamingos ta ci gaba da kai hare-hare babu kakkautawa.
Kwallaye sun ci gaba da zuwa a karshen wasan, yayin da Ohunene Sunday ta zura kwallo ta uku a minti na 83.
Oluebube Umejiaku ta ci ta hudu, sannan daga karshe Ayomide Rotimi ta kara kwallo ta biyar a minti na 94.
Wannan nasara mai girma ta zama tamkar wani babban sako mai karfi ne ga sauran abokan karawar Flamingos a gasar yayin da take kokarin kare kambunta.