A matsayin wani bangare na ayyukan dake nuna Ranar Tsaftace Muhalli ta Duniya ta shekarar 2026, kungiyoyi, kungiyoyin farar hula, shugabannin al’umma, da masu aikin sa-kai sun hada karfi da karfe domin tsaftace sassan jihar Kaduna gami da fadakar da jama’a game da kiyaye muhalli.
Ana gudanar da Ranar Tsaftace Muhalli ta Duniya ta shekarar 2026 ne karkashin taken “Daga Tsaftataccen Kofon Abinci Zuwa Tsaftataccen Birni” (From Clean Plates to Clean Cities), wanda ke bayyana bukatar rage asarar abinci da kuma inganta al’ummomi masu tsafta, koshin lafiya, da dorewa.
Yayin da take jawabi a lokacin aikin tsaftace muhallin a Kaduna, Habiba Suleman, wadda ita ce ta shirya ayyukan Ranar Tsaftace Muhalli ta Duniya ta 2026 a Kaduna kuma Shugabar kungiyar Plogging Nigeria ta Jami’ar Jihar Kaduna (KASU), ta bayyana cewa kungiyoyi da dama ne suka halarci aikin da nufin tsaftace kewayen Kaduna da kuma karfafa gwiwar mazauna garin su dauki nauyin kula da muhallinsu da muhimmanci.
Ta ce halartar kungiyoyin farar hula, shugabannin al’umma, da masu aikin sa-kai yana nuna muhimmancin hadin gwiwa wajen magance gurbacewar muhalli sanadiyyar tulin shara da sauran kalubalen muhalli dake damun al’ummomi.
A cewarta, aikin ya wuce batun kwashe shara kawai, domin an tsara shi ne kuma da nufin wayar da kai sosai game da zubar da shara cikin gaskiya da rikon amana, sake sarrafa shara (recycling), da kuma bukatar tsaftace wuraren taruwar jama’a.
- Brentford ta lallasa Chelsea da ci 3-0 a wasan mako na biyar
- Yadda Amusan ta samu dala 35,000 a Gasar Athlos 2026 na London
Haka kuma, yayin da yake jawabi, Shugaban Bangaren Sadarwa da Tsare-tsare na kungiyar Masu Rahoton Sauyin Yanayi na Afirka (African Climate Reporters – ACR), Ibrahima Yakubu, ya ce kungiyar ta ACR ta shiga aikin tsaftace muhallin ne a matsayin wani bangare na alkawarinta na kiyaye muhalli da ayyukan yaki da sauyin yanayi.
Ya bayyana cewa kafafen yada labarai suna da muhimmiyar rawar da zasu taka wajen ilimantar da jama’a game da sarrafa shara, gurbacewar muhalli, da kalubalen muhalli dake da alaka da sauyin yanayi.
Ibrahima Yakubu ya jaddada cewa kiyaye tsaftar Kaduna yana bukatar hadin gwiwa da daukar nauyi daga hukumomin gwamnati, kungiyoyin farar hula, shugabannin al’umma, ‘yan kasuwa, kafafen yada labarai, da mazauna garin baki daya.
Ya kara da cewa, kungiyar African Climate Reporters zata ci gaba da inganta aikin jarida na sauyin yanayi da muhalli a matsayin makami na fadakarwa, karfafa sauyin dabi’u, da kuma tattara al’ummomi domin daukar mataki da nufin yaki da lalacewar muhalli.