Tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Alhaji Ibrahim Idris, ya rasu.

Jaridar Blueprint ta ruwaito cewa Idris ya rasu ne ranar Lahadi, 20 ga Satumba, 2026, a Birtaniya, yana da shekaru 77 a duniya.

Ko da yake har yanzu bayanan da suka shafi rasuwar ba su cika bayyana ba, majiyoyin iyalan marigayin sun ce Idris ya dade yana fama da rashin lafiya.

A halin da ake ciki, Gwamnan Jihar Kogi mai ci, Ahmed Usman Ododo, ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan tsohon gwamnan.

A cikin sakon ta’aziyyar, Ododo ya bayyana marigayin a matsayin mutum da ya bayar da gudunmawa mai ma’ana a fagen siyasa da kasuwanci.

Gwamnan ya kuma tuna ganawarsa ta karshe da marigayin a watan Maris na 2024, lokacin da ya kai ziyara tare da wasu masu ruwa da tsaki kan harkokin siyasa daga Karamar Hukumar Omala.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *