Tawagar Falconets ta Najeriya ta yi ban kwana da Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata ‘yan ƙasa da shekaru 20 ta 2026 da ake bugawa a Poland, bayan shan kaye da ci 1-0 a hannun Columbia a wasan kwata-fainal da suka buga ranar Lahadi a Łódź.
Tawagun biyu sun buga wasa mai zafi a rabin farko, sai dai babu wadda ta iya zura ƙwallo a ragar abokiyar karawarta duk da irin damarmaki da suka samu musamman ’yan wasan Falconets.
Rabi na biyu na wasan ya kasance cikin tashin hankali da nuna karfin jiki da kuma ɗaukar matakan ladabtarwa, yayinda da Sintia Cabezas da Juana Ortegon na Colombia, da kuma Rebecca Adegbemile ta Najeriya duk suka samu katin gargadi.
-
Ƙwallaye uku da Raphinha ya zura sun baiwa Barcelona nasarar ci 3-1 a kan Sevilla
-
Salah ya zura ƙwallaye uku, yayin da Trabzonspor ta ragargaji Galatasaray
-
Brighton ta ragargaji Arsenal da ci 3-0
Wasan ya juya wa Najeriya baya a minti na 77, lokacin da aka baiwa Kafayat Mafisere jan kati kai tsaye saboda ƙetar da ta yi wa Samantha Rodriguez na Columbia.
Rage yawan ’yan wasan Falconets ya janyo musu cikas da fargaba, yayin da ƙoƙarinsu na neman cin ƙwallo ya zama musu da wahala.
A ƙarshe, ’yar wasan Columbia Valerin Loboa, ce ta zura ƙwallon da ya kawo ƙarshe tafiyar Falconets a gasar a minti na biyu na ƙarin lokaci.