Hukumar Tsaron farin kaya (NSCDC) ta ce ta tsare jami’anta 24 a hedikwatar hukumar da ke Abuja, bisa zargin alaka da mutuwar mutane 33 da ake zargin masu hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba ne a Jihar Neja.
A cikin wata sanarwa da Jami’in Hulda da Jama’a na kasa na hukumar, ACC Babawale Afolabi, ya fitar, ya ce adadin jami’an da aka tsare ya karu daga 21 zuwa 24, bayan gano wasu jami’ai uku da ake zargi suna da hannu cikin lamarin.
Sanarwar ta ce tun ranar 17 ga Satumba, 2026, aka kai jami’an Rundunar NSCDC ta Jihar Neja da ake zargi zuwa hedikwatar kasa da ke Abuja, inda ake gudanar da tambayoyi da matakan ladabtarwa na cikin gida.
- ‘Yan uwan mijin da ake zargin matarsa ta kashe shi saboda zai mata kishiya na neman a yi adalci
- Tsohon Gwamnan Kogi Ibrahim Idris ya rasu a Birtaniya
- NDC ta nesanta kanta da kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na OK Movement
Hukumar ta ce ana gudanar da binciken ne domin tabbatar da cewa jami’an da ake zargi za su kasance a hannun Kwamitin Bincike Mai Zaman Kansa da Shugaban Kasa ya kafa, da sauran kwamitocin da ke binciken lamarin, domin daukar matakin da ya dace.
Kwamandan Janar na NSCDC, Farfesa Ahmed Abubakar Audi, ya ce hukumar ba za ta lamunci rashin da’a da amfani da karfi fiye da kima ko duk wani aiki da zai tauye hakkin ‘yan kasa ba.
A matsayin nuna jimami kan mutuwar mutanen 33, Kwamandan Janar din ya kuma bayar da umarnin sauke tutar NSCDC zuwa rabi a dukkan rassan hukumar na tsawon kwanaki uku, daga ranar Lahadi, 20 ga Satumba, 2026.
Daga cikin jami’an da aka tsare akwai Kwamandan NSCDC na Jihar Neja, Commandant Subaru Siyaka Aniviye, da shugabannin sassan leken asiri da bincike, ayyuka da harkokin shari’a, da wasu jami’ai.
