Sojojin ‘Operation ENDURING PEACE’ sun ceto mutane biyu da aka yi garkuwa da su, tare da kama mutane 12 da ake zargi da hannu a ayyukan garkuwa da mutane a wasu sassan jihar Filato.

A cikin wata sanarwa da Jami’in Yada Labarai na Operation ENDURING PEACE, Kyaftin Chinonso Polycarp Oteh, ya fitar, ya ce an gudanar da ayyukan ne a ranar Asabar, 19 ga Satumba 2026, bisa bayanan sirri kan ayyukan masu garkuwa da mutane a yankin Rayfield da wasu sassan karamar hukumar Jos North.

Sanarwar ta ce sojojin sashe na 1, da aka jibge a Lamingo, sun kai samame maboyar masu aikata laifuka a Shere, Gwafan da Maza Hills, inda suka kama mutane 11 da ake zargi da kasancewa mambobin wata kungiyar masu garkuwa da mutane.

A cewar rundunar, bayanan da aka samu daga wasu mutane biyu da aka yi garkuwa da su a Gwafan Community ranar 18 ga Satumba sun taimaka wajen ci gaba da binciken.

Rundunar ta ce yayin binciken farko, wadanda aka ceto sun gane mutane uku daga cikin wadanda aka kama, inda suka bayyana su a matsayin wadanda ake zargi da kasancewa cikin kungiyar da ta yi garkuwa da su.

A wani ci gaban da ya shafi aikin, sojojin Sector 3 da ke aiki a karamar hukumar Bassa sun gudanar da wani samame da misalin karfe 6 na yammacin ranar 19 ga Satumba, inda suka kwato bindiga kirar gida guda tare da kama wani mutum da ake zargi.

Rundunar ta ce sojojin na ci gaba da mamaye yankin domin gano da kuma kama sauran mambobin kungiyar.

Haka kuma, sojojin sashe na 8 da aka jibge a karamar hukumar Mangu sun gudanar da sintirin tabbatar da zaman lafiya a hanyar Tul–Ntam–Angwan Mata–Deng-Deng.

A yayin sintirin, an kama wani mutum da ake zargi a yankin Water Board, bayan da ya yi yunkurin boye wani makami yayin da ya ga sojojin.

Binciken da aka gudanar a kansa ya kai ga kwato wata bindiga kirar gida mai sarrafa kanta, harsasai tara na 7.62mm Special da kuma wayar salula guda.

Rundunar ta ce dukkan wadanda aka kama suna tsare kuma ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano sauran mambobin kungiyar da kuma gudanar da wasu ayyuka na musamman domin kama wadanda suka tsere.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *