Iran ta ce duniya za ta yi matuƙar mamakin irin sabbin makaman da take shirin amfani da su idan har Amurka ta sake kai mata hari.
Rahotanni sun ce hukumomin Iran, sun yi wannan gargaɗin ne yayin da wasu ’yan majalisar dokokin ƙasar suka gabatar da wani kudirin doka na janye Iran daga yarjejeniyar hana ta mallakar makaman nukiliya.
A halin da ake ciki kuma, an bayar da rahoton mutuwar mutane huɗu a lardin Al-Jawf na Yemen, yayin da yaƙi tsakanin mayaƙan Houthi da dakarun Saudiyya ke cigaba da kai hare-hare.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da fuskantar tashin hankali a yankin Gabas ta Tsakiya, musamman kan babbar hanyar jiragen ruwan Hormuz.
Hukumar kula da harkokin teku ta Birtaniya ta ce barazanar tsaro a mashigar ruwan na cigaba da tsanananta, idan akayi la’akari da raguwar adadin jiragen ruwan da ke wucewa ta mashigar a kullum. Adadin da majiyar sojin Amurka ta tabbatar.
A wani labarin kuma, Firayiministan Qatar, Sheikh Mohammed bin Abdulrahman bin Jassim Al Thani, ya yi kira da a samar da ƙarin tsaro na bai ɗaya a yankin Gulf, ƙarƙashin tsarin da ya ginu kan mutunta ikon kowace ƙasa da kuma hana wata ƙasar zama barazana ga wata.
Sai dai duk da irin waɗannan kiraye-kiraye, barazanar Iran ta nuna cewa har yanzu akwai rashin jituwa tsakanin Tehran da Washington, lamarin da ka iya ƙara dagula barzanar tsaro a yankin.