Ministan Babban Birnin Tarayya, FCT, Nyesom Wike, ya ce zai bayyana wa ’yan Najeriya dalilin da ya sa wasu ’yan siyasa ke adawa da ƙungiyar siyasa ta Rainbow Coalition.
Wike ya yi wannan bayani ne yayin da yake martani kan zargin da wasu mambobin Ƙungiyar Gwamnonin Masu Ci Gaba suka yi cewa Rainbow Coalition na da nufin kawo cikas ga jam’iyyar APC da kuma raunana matsayin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Ministan ya musanta wannan zargi, yana mai cewa babban abin da ya dame shi shi ne ganin Shugaba Tinubu ya sake lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2027. Ya ce ya bayyana wannan matsaya tun farko, kuma zai yi cikakkencikakken bayani ga ’yan Najeriya kan abin da yake ganin shi ne dalilin adawar da ake yi wa Rainbow Coalition.
Wike ya ce bai fahimci yadda ƙungiyar za ta kawo cikas ga APC ba, yana mai cewa ba su je wajen wani ɗan jam’iyya domin su hana shi goyon bayan Shugaba Tinubu ba.
A cewarsa, abin da ake yi shi ne haɗa ’yan jam’iyyun siyasa da masu ra’ayi iri ɗaya, ciki har da waɗanda ba ’yan APC ba, domin su goyi bayan Shugaba Tinubu.
Ya kuma yi watsi da zargin cewa Rainbow Coalition wata hanya ce da yake amfani da ita domin shirya kansa ga takarar shugaban ƙasa a shekarar 2031.
Wike ya ce bai kamata a fara tsara irin wannan siyasa tun yanzu ba, domin ba a san abin da zai faru nan gaba ba.
Ministan ya ce ’yan siyasa su fara fatan samun rai da lafiya kafin su fara tsara abin da zai faru a shekarar 2031, yana mai jaddada cewa makomar siyasa tana ƙarƙashin ikon Allah.
Wike ya ce zai yi karin bayani a wani shirin talabijin da aka tsara, inda ya yi alkawarin bayyana cikakkun bayanai kan dalilin da ya sa ake samun suka da adawa ga Rainbow Coalition.