Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya tsawaita hutun aikinsa da wasu ’yan kwanaki, inda ake sa ran zai dawo Najeriya a karshen wannan mako.
Shugaba Tinubu ya bar Najeriya a ranar 30 ga Agusta zuwa birnin Landan na Birtaniya domin fara hutun aikinsa.
- Wike ya ce za a kammala manyan ayyukan Abuja zuwa Janairu 2027
- NAF ta fara sayen jirage masu saukar ungulu 12 kirar AH-1Z Viper
- Zuwan Blueprint Radio cigaba ne ga Najeriya–Ministan Watsa Labarai
A cewar sanarwar da Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Yaɗa Labarai da Dabarun Sadarwa, Bayo Onanuga, ya fitar, Shugaba Tinubu ya ci gaba da kasancewa cikin tuntuba da Najeriya tun bayan tafiyarsa, yana kuma jagorantar harkokin gwamnati daga inda yake.
Bayan shafe mako guda a Landan, shugaban ya zarce zuwa birnin Paris na Faransa, inda ya gana da Shugaban Faransa Emmanuel Macron da ɗan kasuwa Vincent Bolloré, wanda ƙungiyar kamfanonin kafafen yaɗa labarai ta ƙunshi Canal+, Multichoice da Universal Music Group.