Ma’aikatan gwamnati a Najeriya sun bai wa gwamnatin tarayya wa’adin zuwa 30 ga Satumba, 2026, da ta gaggauta daukar matakan magance matsananciyar tsadar rayuwa da ma’aikata da wadanda suke dogaro da su ke fuskanta a fadin ƙasar.

Ma’aikatan, karkashin Ƙungiyar Haɗin Kan Majalisar Tattaunawar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya (JNPSNC), ɓangaren ƙungiyoyin kwadago, sun bukaci gwamnatin tarayya ta daidaita farashin man fetur (PMS) zuwa Naira 500 kan kowace lita.

Sun bayyana bukatun ne a cikin wata wasiƙa da suka aikewa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, inda suka yi gargadin cewa matsin tattalin arzikin da ake fuskanta a faɗin ƙasar na haifar da tashin hankali tsakanin ma’aikata da sauran ‘yan Najeriya, wanda ka iya haifar da yanayin da ba a so.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa wannan kira na ma’aikatan ya zo ne kwanaki kaɗan bayan shugabancin Majalisar Ƙwadago ta Najeriya (NLC) ya buƙaci gwamnatin tarayya ta gaggauta amincewa da tallafin gaggawa da kuma ƙarin albashi ga ma’aikata a faɗin ƙasar.

A ranar Larabar da ta gabata ne NLC ta yi kira ga gwamnati da ta samar da matakan rage radadin da tashin farashin man fetur ke haifarwa, tare da tabbatar da sayar da ɗanyen mai ga matatun man cikin gida da Naira.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *