Taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 81, ya kankama a hukumance ranar Talata, 22 ga Satumba 2026, a hedikwatar Majalisar da ke birnin New York
Shugabannin ƙasashe, gwamnatoci da jami’an diflomasiyya daga sassan duniya ne suka hallara domin tattauna manyan matsalolin da suka shafi duniya.
Taken taron na bana shi ne “Maido da amana da sauyi: Majalisar Ɗinkin Duniya da ke samar da mafita ga kowa.”
Tattaunawar shugabannin duniya za ta mayar da hankali kan batutuwan da suka shafi zaman lafiya, ci gaba mai ɗorewa da ƙarfafa haɗin gwiwar ƙasashe.
Batun makomar Falasɗinu na daga cikin manyan batutuwan da ake sa ran za su mamaye taron.
Shugaban Falasɗinu Mahmoud Abbas zai sake gabatar da jawabi ta intanet, sakamakon rashin samun biza daga kasar Amurka, yayin da wasu shugabannin yankin, ciki har da Shugaban Iran Masoud Pezeshkian, za su halarci taron da kansu.
Ministan Harkokin Wajen Bangladesh, Dr Khalilur Rahman, ne ke jagorantar zaman karo na biyu a tarihi da Bangladesh ke riƙe da shugabancin babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya, bayan Humayun Rashid Choudhury wanda ya jagoranci zaman karo na 41 a shekarun 1986 zuwa 1987.
Haka kuma, ana sa ran batun zaɓen sabon Sakatare-Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya zai kasance cikin abubuwan da za a tattauna a taron, yayin da wa’adin Sakatare-Janar na yanzu, António Guterres, zai ƙare ne a ranar 31 ga Disambar 2026.
Ana sa ran Firayminista Tarique Rahman na Bangladesh zai gabatar da jawabi a ranar Alhamis 24 ga Satumba kan manufofin ƙasar sa a fagen hulɗa da ƙasashen duniya.
Shugabanni da jami’ai za su tattauna batutuwan da suka haɗa da hauhawar ruwan teku, cimma muradun ci gaba mai ɗorewa, da kuma hanyoyin ƙarfafa haɗin gwiwa domin magance matsalolin duniya.