Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta Amnesty International ta buƙaci gwamnatin Najeriya da ta gudanar da bincike mai zaman kansa, cikin adalci da gaskiya kan zarge-zargen take haƙƙin ɗan Adam da aka aikata a yankin Kudu maso Gabas tsakanin shekarun 2016 zuwa 2025.

Ƙungiyar ta yi wannan kira ne a wani gangamin wayar da kai da nuna goyon baya da ta gudanar a Awka na jihar Anambra, domin neman adalci ga mutanen da rikicin yankin ya shafa.

Da yake gabatar da rahoton ƙungiyar, Maurice Chukwu ya ce daga watan Janairun 2021 zuwa Disamban 2024, yankin ya fuskanci kashe-kashe ba bisa ƙa’ida ba da hare-hare da azabtarwa da ɓacewar mutane da kama mutane ba bisa ƙa’ida ba da kuma tauye ‘yancin zirga-zirga.

Yankin Kudu maso Gabas ya jima yana fuskantar hare-haren ta’addacci duk da ƙoƙarin da hukumomin tsaro ke yi na shawo kan matsalar.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *