Jam’iyyar APC mai mulki ta caccaki ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na ADC, Rotimi Amaechi, kan kalaman da ya yi cewa tsadar magunguna sakamakon manufofin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta sa ya kasa sayen maganin mahaifiyarsa kafin rasuwarta.
A cikin wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labarai na APC na ƙasa, Felix Morka, ya fitar a Abuja ranar Lahadi, jam’iyyar ta ce kalaman Amaechi sun sanya tambaya kan yadda zai iya gudanar da rayuwarsa ba tare da dogaro da kuɗin gwamnati ba.
APC ta tuna da cewa Amaechi ya riƙe manyan mukamai a gwamnati, ciki har da Shugaban Majalisar Dokokin Rivers, Gwamnan jihar da kuma Ministan Sufuri, kafin ya koma ADC a matsayin abokin takarar shugaban ƙasa na 2027.
- An kashe mutane uku a Minna sakamakon zanga-zangar ‘yan daba a jihar
- Najeriya za ta kara da Spaniya, da Turkiyya da Masar a gasar…
Jam’iyyar ta kuma yi amfani da kalaman Amaechi na baya-bayan nan da ya ce ya shiga matsin tattalin arziki har matarsa ke taimaka masa wajen ciyar da shi, tana mai cewa hakan na nuna rashin iya dogaro da kansa bayan barin gwamnati.
APC ta bayyana Amaechi da kalamai masu zafi, tana mai cewa bai kamata ya nemi kujerar mataimakin shugaban ƙasa ba idan har ba zai iya ɗaukar nauyin kansa da iyalinsa ba bayan barin mulki.
Sai dai kalaman APC sun zo ne bayan Amaechi ya zargi manufofin gwamnatin Tinubu da tsadar magunguna da ya ce ta sa kula da mahaifiyarsa ta yi masa wahala. Mahaifiyarsa, Mary Amaechi, ta rasu a watan Yuli tana da shekara 89.