Shugaban Rundunar Sojin Ƙasa, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya shiga cikin manyan jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki a wani babban taron ƙasa da ƙasa kan ƙarfafa ayyukan Rundunar Hadin Gwiwa ta Ƙasashe da ke Yankin Tafkin Chadi (MNJTF).
An gudanar da taron ne a National Defence College da ke Abuja, inda aka tattauna hanyoyin inganta haɗin gwiwar tsaro, musayar bayanan sirri, samar da kayan aiki, kuɗaɗen gudanar da ayyuka da kuma daidaita ayyukan sojojin ƙasashen da ke cikin MNJTF.
- Akpabio ya wakilci Najeriya a taron IPU na 153 a Tanzania
- Hope Uzodimma ya nemi ’yan Najeriya su ci gaba da mara wa Tinubu baya
Taron ya haɗa manyan jami’an tsaro daga Najeriya da ƙasashen Nijar, Kamaru, Chadi da Benin, da wakilan Tarayyar Afirka, Lake Chad Basin Commission da sauran abokan hulɗa na ƙasa da ƙasa.