Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya jagoranci tawagar Najeriya zuwa taron 153 na Kungiyar Majalisun Duniya (IPU), da ake gudanarwa a Arusha, Tanzania.

A yayin bude taron, Shugabar Tanzania, Samia Suluhu Hassan, ta jaddada muhimmancin ƙarfafa majalisu, tabbatar da rikon amana da zurfafa haɗin gwiwar ƙasashe domin magance ƙalubalen da duniya ke fuskanta.

Taron na wannan shekarar na karkashin taken “Inganta shugabanci nagari da ƙarfafa al’umma ta hanyar haɗin kai, amana da samar da dama ga kowa.”

Akpabio ya ce halartar Najeriya na ba ƙasar damar ƙara ƙarfafa dangantakar diflomasiyyar majalisa, da kuma bayar da gudunmawa wajen tattaunawar da za ta inganta shugabanci nagari, zaman lafiya da ci gaba mai ɗorewa.

Ya ce a yayin da ƙasashe ke fuskantar yaƙe-yaƙe, matsalolin tattalin arziki da sauyin yanayi, haɗin gwiwa tsakanin majalisun duniya ya zama mafi muhimmanci wajen nemo hanyoyin magance waɗannan matsaloli.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *