Ɗan takarar Gwamna na jam’iyyar ADC a Jihar Ekiti, Deji Bejide, ya sha kaye a Mazaɓar sa, bayan da Gwamna mai ci, Biodun Oyebanji na jam’iyyar APC, ya samu rinjaye.
Sakamakon da aka bayyana ya nuna cewa jam’iyyar APC ta samu ƙuri’u 140, yayin da ADC ta samu ƙuri’u 37.
-
Ƙananan Hukumomi 16 na Jihar Ekiti da zaɓen gwamna ya gudana cikin su
-
Zaben EKiti: Dan Takarar Gwamna na jam’iyyar PDP Dakta Wole ya zargi ana tsoratar da masu kada kuri’a
Sauran jam’iyyun da suka samu ƙuri’u a mazaɓar sun haɗa da AAC mai ƙuri’u Uku, da kuma PDP mai ƙuri’u Biyu.
Sakamakon ya nuna cewa Gwamna Oyebanji na APC ke da rinjaye a mazaɓar Deji Bejide, kawo lokacin da ka kammala tattara ƙuri’u da yammacin ranar Asabar.