An amince da rabon kuɗin ne a taron kwamitin na watan Nuwamba 2026 da aka gudanar a Abuja, ƙarƙashin jagorancin Ministan Kuɗi kuma mai kula da tattalin arzikin ƙasa, Taiwo Oyedele.
Kuɗin ya fito ne daga jimillar kuɗaɗen shiga da suka kai Naira tiriliyan 3.812.
Daga cikin kuɗin da aka raba, Gwamnatin Tarayya ta samu Naira biliyan 856.06, gwamnatocin jihohi kuma sun samu Naira biliyan 809.91, yayin da ƙananan hukumomi suka samu Naira biliyan 568.70.
- Ranar Maza ta Duniya: Muhimmiyar rawar da Maza ke takawa wajen cimma burin Mata
- An ceto wata babbar kunkuru mai zuwa bakin teku domin yin ƙwai a Ghana
Haka kuma, jihohin da ke samar da man fetur sun samu ƙarin Naira biliyan 206, bisa tsarin kashi 13 cikin 100 na rabon kuɗaɗen da ake bai wa jihohin da ke samar da man fetur.
Kwamitin ya bayyana cewa kuɗaɗen shiga na doka da aka samu a watan Oktoba sun kai Naira tiriliyan 2.999, wanda ya nuna raguwar Naira biliyan 97.3 idan aka kwatanta da na watan Satumba. Haka kuma, kuɗaɗen harajin VAT sun ragu daga Naira biliyan 816.9 a watan Satumba zuwa biliyan 812.4 a watan Oktoba.
Rahoton ya ƙara da cewa kuɗaɗen harajin kaya da na kwastam sun samu ɗan ƙaruwa, yayin da kuɗaɗen shiga daga man fetur, harajin shigo da kaya da kuma harajin kamfanoni suka ragu.