Matakin ya biyo bayan yaɗa wani sharhi da kuma hoton zanen barkwanci da hukumomin Guinea suka ɗauka a matsayin cin mutuncin Shugaban Ƙasar, Mamadi Doumbouya.
Hukumar ta ɗauki matakin ne bayan abubuwan da gidan talabijin ɗin ya yaɗa, waɗanda suka jawo ce-ce-ku-ce tsakanin ƙasashen biyu.
- Ranar Maza ta Duniya: Muhimmiyar rawar da Maza ke takawa wajen cimma burin Mata
- FAAC ta raba Naira tiriliyan 2.44 ga gwamnatocin Najeriya
Dakatarwar na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan da hukumomin Guinea suka kori sama da mutum 150,000 da ke haƙar zinare a ƙasar, waɗanda mafi yawansu ’yan asalin Burkina Faso ne.
Guinea ta ce korar masu haƙar zinaren na da nasaba da kare muhalli da kuma dakile barazanar tsaro da take ganin suna iya tasowa daga ayyukansu.
Matakan biyu sun zo ne a daidai lokacin da ake samun takun-saka tsakanin ƙasashen biyu, musamman kan yadda ake gudanar da ayyukan haƙar ma’adinai da kuma abubuwan da ake yaɗawa a kafafen yaɗa labarai.