Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya (FIFA) ta tabbatar a hukumance da sunayen mambobin kwamitin rikon kwarya na Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya (NFF).
FIFA ta nada Mista Sampson Ebomhe a matsayin shugaban kwamitin, tare da tsohon dan wasan Super Eagles, Daniel Amokachi, da wasu mutane uku.
An bayyana nadin ne a cikin wata wasika mai kwanan wata 18 ga watan Nuwamba, 2026, wadda FIFA ta aika wa babban sakataren NFF, Mista Emmanuel Ikpeme.
-
Manchester United ta sallami Michael Carrick daga aikin kocin tawagarta
-
Najeriya ta kammala gasar Olympics na matasa na Dakar 2026 da tarihi mai kyau
-
Najeriya ta lashe Gasar Cin Kofin Duniya bayan doke Japan 2-1
Nadin ya biyo bayan matakin da ofishin majalisar FIFA ya dauka a ranar 22 ga Oktoba, 2026, na kafa kwamitin rikon kwarya domin tafiyar da harkokin kwallon kafa a Najeriya, bayan shawarwari da Hukumar Kwallon Kafa ta Afirka (CAF).
Sauran mambobin kwamitin sun hada da Dr Joe Abah, da Mista Godwin Enakhena, da Misis Amina Yerima da kuma tsohon dan wasan Najeriya, Daniel Amokachi.
Ana sa ran mambobin kwamitin guda biyar za su fara gudanar da ayyukansu nan take.
Sai dai FIFA ta bayyana cewa nadin nasu na jiran tantance cancantarsu daga kwamitin tantancewa na hukumar, bisa ka’idojin tafiyar da harkokin FIFA.
Hukumar ta kuma jaddada cewa babu wani daga cikin mambobin kwamitin da zai cancanci tsayawa takara a kowane mukami a zaben NFF mai zuwa, ko da kuwa daga baya aka cire shi daga kwamitin ko kuma ya yi murabus.
FIFA ta kuma bayyana cewa tana da ikon, tare da tuntubar CAF, janye nadin duk wani mamba na kwamitin ko kuma nada karin wasu mambobi idan bukatar hakan ta taso.