Dan wasan gaba na Real Madrid, Vinícius Júnior.

Real Madrid na neman a biya ta aƙalla Yuro miliyan 150 ($164.5m) kafin ta amince da sayar da Vinícius Júnior, a daidai lokacin da ake samun rahotannin cewa Arsenal ta sake nuna sha’awar ɗaukar ɗan wasan. (Majiyar labari: Josep Pedrerol).

Lamine Yamal ya nuna adawa mai ƙarfi da tunanin Barcelona na karɓar tayin Yuro miliyan 120 ($131.6m) daga Chelsea domin sayen Fermín López. Wannan ya samo asali ne daga kyakkyawar alaƙar da ke tsakaninsu, a filin wasa da wajen filin wasa, kasancewar sun fito daga makarantar horas da matasa ta Barcelona tare. (Majiyar labari: El Nacional).

Bruno Fernandes da Virgil van Dijk, waɗanda su ne kyaftin ɗin Manchester United da Liverpool bi da bi, sun fuskanci ƙin amincewa daga Hansi Flick. Kocin Barcelona ɗin bai ga dacewar ƙungiyar ta yi la’akari da ɗaukar su kyauta ba a lokacin kasuwar musayar ‘yan wasa ta bazara mai zuwa. (Majiyar labari: El Nacional).

Liverpool ta fara tattaunawar sabunta kwantiragi da Alexis Mac Allister, bayan a baya ta dakatar da batun sabon kwantiragi da ɗan wasan tsakiyar Argentina ɗin, wanda ake alakanta shi da komawa Real Madrid. (Majiyar labari: César Luis Merlo).

Arsenal ta bayyana Carlos Forbs, na Club Brugge a matsayin ɗan wasan da ya dace ya zama madadin Bukayo Saka, inda ake sa ran kuɗin sayensa zai kai kusan Yuro miliyan 30 ($32.9m) (Majiyar labari: Fichajes).

Yayin da Liverpool ta karkata hankalinta kan Lamine Camara na Monaco, Chelsea na da kyakkyawan fata za ta iya kammala cinikin Alex Scott na Bournemouth kan fam miliyan 90 ($118.3m). (Majiyar labari: Si Phillips).

Liverpool, Chelsea da Real Madrid na cikin ƙungiyoyin da ke sha’awar ɗaukar Martín Zubimendi na Arsenal, wanda ba ya samun isasshen lokacin buga wasa. Arsenal ta sanya kuɗin sayensa a kan Yuro miliyan 70 ($76.8m). (Majiyar labari: AS).

Juventus da Chelsea duk suna sha’awar ɗaukar Maxi Araújo, ɗan wasan baya na gefen hagu na Sporting CP. (Majiyar labari: A Bola).

An yi hasashen cewa Beşiktaş za ta iya tuntuɓar Manchester United domin neman ɗaukar Amad Diallo, lamarin da ya zo da mamaki. (Majiyar labari: Sabah).

Liverpool ta nuna sha’awarta a hukumance ta sayen Arthur Dias, ɗan wasan Club Athletico Paranaense. Ana kimanta kuɗin sayensa da Yuro miliyan 25 ($27.4m). (Majiyar labari: El Nacional).

Manchester City ta sanya kuɗin sayar da Rayan Aït-Nouri a kan fam miliyan 30 ($39.4m), yayin da Barcelona ke nuna sha’awar ɗaukar ɗan wasan. (Majiyar labari: Football Insider).

Baya ga neman Fermín López, Chelsea na shirin bayar da Yuro miliyan 60 ($65.8m) domin sayen Jules Koundé. (Majiyar labari: El Nacional)

Barcelona na bibiyar Juan Rodríguez, ɗan wasan baya na Cagliari kuma ɗan ƙasar Uruguay, a matsayin wanda zai iya magance matsalar tsaron gidanta. (Majiyar labari: El Observador).

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *