Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya buƙaci Ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewa (ACF) da Ƙungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa da sarakunan gargajiya da Majalisar Dokoki ta Ƙasa su haɗa kai wajen samar da dokar da za ta kawo ƙarshen tsarin almajirci a faɗin Nijeriya.

Gwamna Sule ya bayyana hakan ne yayin taron bunƙasa ƙwazon aiki na ma’aikata a Arewacin Nijeriya, wanda Gidauniyar Tunawa da Sir Ahmadu Bello ta shirya tare da haɗin gwiwar Ƙungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa a Abuja.

Ya ce tsarin almajirci ya zama ɗaya daga cikin manyan abubuwan da ke haddasa ƙaruwar yara marasa zuwa makaranta da matsalar rashin tsaro a yankin Arewa.

Ya tunatar da cewa a shekarar 2020, shi da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, sun jagoranci wani shiri na tantance almajirai tare da mayar da su jihohin da suka fito.

Ya ce a lokacin Jihar Nasarawa tana da almajirai sama da 200,000, waɗanda aka mayar zuwa jihohin Jigawa da Sokoto da Kano da sauran jihohi.

Ya bayyana cewa a halin yanzu Jihar Nasarawa na da yara 430,000 da ba sa zuwa makaranta, ciki har da maza 179,000 da mata 251,000.

Ya ce daga cikin yara miliyan 18 da ba sa zuwa makaranta a Nijeriya, miliyan 15 suna jihohin Arewa, lamarin da ya ce na buƙatar matakin gaggawa.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *