Gwamnatin Jihar Filato ta bayar da umarnin buɗe makarantun firamare da sakandare na gwamnati da masu zaman kansu a faɗin jihar a ranar Litinin, 14 ga Satumbar, 2026, tare kuma da ƙarfafa matakan hana yaɗuwar cutar mashaƙo.
Gwamnatin ta ce ta yanke wannan shawarar ne sakamakon aiwatar da matakan kariya da na kiwon lafiya domin daƙile yaɗuwar cutar mashaƙo da ake zargi a wasu sassan jihar.
A ranar Asabar da ta gabata, gwamnatin ta ba da umarnin rufe dukkan makarantun firamare da sakandare na gwamnati da masu zaman kansu a faɗin jihar na wucin gadi.
- Cutar mashako ta halaka mutum 13 a Jihar Yobe
- An kai wa Sheik Musa Lukuwa hari a masallaci
- NNPC ta ƙaddamar da gidan mai na zamani a Abuja
A cikin wata sanarwar da Kwamishinan Yaɗa Labarai da Sadarwa ta jihar, Joyce Ramnap, ta sanya wa hannu ranar Jumma’a, gwamnatin ta ce hakan “na daga cikin kudurin gwamnati na tabbatar da kare lafiya da jin daɗiin ɗialibai, da malamai da kuma sauran mambobin al’ummar makaranta, domin tabbatar da ci gaba a fannin ilimi.”
A cewar gwamnatin, ta ɗiauki matakan rufe makarantu ne a can baya don ƙarfafa fannin lafiya da tsarin magance cututtuka.
Gwamnatin ta tabbatar wa iyaye, da masu kula da yara, da masu makarantu da kuma masu gudanar da su cewa an ɗauki matakan da suka dace kafin buɗe makarantun.
Gwamnatin ta kuma ba masu makarantu umarnin su kula da matakan kariya na da kuma kiyaye tsaftar muhalli.
Bugu da ƙari, sanarwar ta ba da shawarar cewa a kai duk wanda ake zargi yanaɗauke da cutar zuwa asibiti don dubawa da kuma samun kulawar kiwon lafiya.