Gwamnatin Tarayya ta ce tana shirin raba na’urorin zamani 400,000 ga matasa, da dalibai, da masu sana’o’i, da ‘yan kasuwa da sauran masu karamin karfi a sassan Najeriya.
Babbar Mataimakiyar Shugaban Kasa kan Ilimin Fasaha da Sana’o’i da Harkokin Kasuwanci, Dakta Abiola Arogundade, ce ta bayyana hakan ranar Alhamis a Abuja. Ta ce shirin na karkashin National Digital Skills and Technical Empowerment Programme (NDSTEP), kuma yana da nufin kara wa ‘yan Najeriya damar samun ilimin fasahar zamani, da koyon sana’o’i da kuma damar fara harkokin kasuwanci.
Ta bayyana hakan ne yayin da take raba kwamfutocin tablet ga ma’aikatan kafafen yada labarai na zamani 70 a wani taron masu ruwa da tsaki da manajojin kafafen yada labarai na zamani.
-
Haɗadɗiyar Daular Larabawa ta dakatar da zirga-zirgar kamfanonin jiragen Iran
-
Shettima ya gabatar da matsayin Najeriya kan sake fasalin Majalisar Dinkin Duniya
Dakta Arogundade ta ce na’urorin za su taimaka wa wadanda za su amfana wajen samun damammaki, nemo abokan hulda da kuma mayar da ilimin sana’o’in da suka koya zuwa hanyar samun abin dogaro da kai. Ta ce waya ko kwamfuta na iya zama wata hanya ta nemo sabbin abokan kasuwan ci da kuma sauya horon sana’a zuwa takardar shedar kwarewa.
Ta ce gwamnatin na kai na’urorin zamani da horar da mutane kan amfani da su zuwa jihohi domin kara yawan wadanda za su shiga harkokin tattalin arzikin zamani da na kasuwanci.
Mataimakiyar shugaban kasar ta ce miliyoyin matasa, da masu sana’o’i, kwararru da kananan ‘yan kasuwa suna da kwarewa, amma rashin samun na’urorin zamani da suka dace na hana su cin gajiyar damammakin da ake da su.
Ta kuma ce kafafen yada labarai na da muhimmiyar rawa wajen tabbatar da cewa shirye-shiryen gwamnati sun isa ga al’umma da wadanda aka tsara za su amfana.
Arogundade ta kuma yi kira da a kara yada labarai kan shirin NPRGS a jihar Oyo, wanda za a gudanar daga ranar 28 ga Satumba zuwa 9 ga Oktoba. Ta ce shirin zai hada da horas da mutane kan dinkin zamani, da Kirkirarriyar basira (AI) da zane-zane ta kwamfuta da kwalliya, kuma ana sa ran fadada shi zuwa dukkan shiyyoyin Najeriya shida a matsayin wani bangare na shirin tallafa wa jama’a daga tushe.