Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a na Najeriya, Mohammed Idris, ya buƙaci ’yan Najeriya su goyi bayan sauye-sauyen da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke aiwatarwa, yana mai cewa matakan na aza harsashin samar da wadata a ƙasar.
Idris ya bayyana hakan ne yayin ziyarar ban girma da Darakta-Janar na ƙungiyar Friends of Tinubu Reforms (FTR), Comrade Agbor Ebipade, ya kai masa domin gabatar da ƙungiyar tare da neman haɗin gwiwar ma’aikatar wajen wayar da kan jama’a game da sauye-sauyen gwamnati, musamman a matakin ƙasa.
Ministan ya bayyana cire tallafin man fetur da haɗa farashin canjin kuɗin waje a matsayin manyan matakan da Tinubu ya ɗauka domin daidaita tattalin arzikin ƙasar.
- Kwana biyar suka rage kafin taron shugabannin kamfanonin da ke hulɗa da NNPC kan tsaro da lafiya
- Shettima ya isa Ekiti domin wakiltar Tinubu wajen rantsar da Oyebanji
- Uzodimma ya jaddada muhimmancin ƙananan hukumomi wajen ci gaban ƙasa
Ya ce akwai lokacin da wasu jihohi ke fuskantar matsalar biyan albashin ma’aikata, amma ya yi iƙirarin cewa hakan ba ya faruwa tun bayan hawansa mulki.
Ya kuma yi nuni da shirye-shiryen gwamnati a fannonin ilimi, noma, tsaro da samar da ababen more rayuwa, ciki har da rancen kuɗin karatu ga ɗalibai da manyan ayyukan tituna.
Idris ya jaddada muhimmancin isar da sahihan bayanai ga jama’a domin su fahimci manufofin gwamnati da amfanin da ake sa ran za su samar.
A nasa jawabin, Ebipade ya ce an kafa ƙungiyar FTR ne domin tallafa wa ajandar Renewed Hope ta Tinubu da ƙarfafa sadarwa tsakanin gwamnati da al’umma.
Ya bayyana cewa ƙungiyar na shirin ƙaddamar da kundin bayanai da zai yi bayanin sauye-sauyen gwamnati ga jama’a, tare da neman goyon bayan ministan wajen aiwatar da shirin.
Ebipade ya kuma gayyaci Idris ya zama babban majiɓincin ƙungiyar, inda ministan ya yi maraba da shirin tare da tabbatar da cewa ma’aikatarsa za ta ci gaba da isar da bayanan manufofi da shirye-shiryen gwamnati cikin harshe mai sauƙin fahimta.