Ƙungiyar Kwadago ta Duniya ILO, ta yaba wa Ministocin Kwadago da Ayyuka na ƙasashen masu karfin tattalin arziki (G7).

Babban Daraktan Ƙungiyar Gilbert Houngbo, yace yabon gwani ya zama dole duba aniyar su Ministcon ta cike gibin rashin aikin yi, a matsayin ginshiƙin gina tattalin arziki mai ɗorewa da kuma tabbatar da adalci a Ƙasashe.

A wasu jawabai da ya gabatar yayin taron Ministocin Kwadago karo 114 da ke gudana a Birnin Geneva, Gilbert Houngbo ya ce dole ne sauye-sauyen tattalin arziki su kasance bisa adalci, zamantakewa da kuma mutunta haƙƙin ma’aikata.

Houngbo ya yi maraba da amincewa da sabon tsarin kasashen, na shimfida Ƙa’idoji domin kaucewa haɗarin bautarwa a bakin aiki.

Daraktan yace ƙasashen sun ƙirƙiro sabbin tsare-tsaren ne, domin taimakawa hukumomin gwamnati da kamfanoni wajen magance cin zarafin ma’aikata a harkar haƙo ma’adanai masu daraja.

Haka kuma, ya yaba da ƙoƙarin inganta tsarin ɗaukar ma’aikatan wucin gadi cikin adalci ta re da kira da a kaucewa  cin zarafi da tauye haƙƙi.

Ministocin sun kuma amince da ƙarfafa haɗin gwiwa wajen bunƙasa ƙwarewa a fannin kirkirarriyar basira (AI) ta hanyar kafa sabuwar cibiyar horar da fasahar (AI) mai suna (G7 AI Training Hub).

Bugu da ƙari, Ministocin sun amince da ci gaba da shirye-shiryen da za su inganta shiga kasuwar ƙwadago, motsin ma’aikata tsakanin ayyuka da yankuna, da kuma ci gaban sana’o’i ga mutane ba tare da banbance shekarunsu ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *