Manchester City ta ci gaba da haskakawa a gasar Premier League bayan ta lallasa Crystal Palace da ci 4–1 a filin wasa Selhurst Park.

Erling Haaland ne ya fara bude wa City kwallayenta a minti na 17, bayan da ya karɓi kyakkyawan cros daga Antoine Semenyo, kafin ya yi amfani da kansa wajen aika ƙwallon cikin raga.

Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, Rayan Cherki ya ƙara wa Manchester City kwallo a minti na 54, inda ya nuna ƙwarewarsa a gaban ragar Palace.

Sai dai mintuna biyu kacal daga baya Crystal Palace ta rage tazarar, bayan bugun daga kai sai mai tsaron gida da Yeremy Pino ya buga sanda kafin ƙwallon ta shiga raga ta bayan Gianluigi Donnarumma.

Manchester City ta sake bayar da tazarar ƙwallaye biyu a minti na 58, lokacin da Cherki ya zura ƙwallonsa ta biyu a wasan.

8Haaland ya kuma kammala wasan da ƙwallonsa ta biyu a minti na 85, bayan Phil Foden ya taimaka masa.

Da wannan sakamakon, Manchester City ta samu nasara ta biyu a jere a farkon kakar Premier League, yayin da sabon kocinta Enzo Maresca ya ci gaba da samun kyakkyawan sakamako tun bayan karɓar ragamar ƙungiyar.

A gefe guda, Crystal Palace ta sha kashi na biyu a jere, bayan da ta fara kakar bana da rashin nasara a hannun Everton.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *